Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da 'Yan Nijar Ke Cewa Kan Soke Yarjejeniyar Soji Da Amurka


Sojojin Amurka
Sojojin Amurka

AGADEZ, NIJAR - Al ‘umma a Jamhuriyar Nijar, musanman jihar Agadas dake arewacin Nijar, yankin da kasar Amurka ke da sansanin soja, na cigaba da bayyana ra’ayoyinsu mabanbanta bayan da gwamnatin mulkin sojan kasar ta bada sanarwar yanke huldar aiyukan soja da Amurka.

Yayin da wasu ke amincewa da ra’ayin ficewar dakarun Amurkan daga Nijar wasu kuma na ganin akwai bukatar gwamnatin mulkin sojin kasar ta duba lamarin ganin yadda dubban yan kasar ke aiki a sansanonin sojin kasar Amurka dake jihar Agadas.

Hakazalika, a yayin da wasu ke yabawa mahukuntan na Nijar wasu kuma na nuna damuwa kan koma bayan da abin zai haddasa a fannoni da dama ficewar dakarun kasar Amurka zai iya kawo gibin da masu tada kayar baya zasu yi kokarin cikewa duba da yadda dakarun kasar Amurka ke tallafawa dakarun Nijar da kayan aiki da kuma yakar yan ta’adda inji.

A baya dai akwai alaka mai karfi tsakanin Amurka da Nijar lamarin da ya sanya ta jibge sojojin ta fiyeda dubu guda a kasar. To sai dai bayan juyin mulkin da sojoji sukayi, al’amurra sun sauya ciki harda kawo karshen alakar dake tsakanin su.

Gwamnatin sojin jamhuriyar Nijar ce ta sanar da soke yarjejeniyar soja ta hadin gwiwa da kasar Amurka wace aka rattaba a shekarar 2012 da nufin yakar kungiyoyin jihadi a yankin Sahel.

A saurari cikakken rahoton Hamid Mahmoud:

Ra'ayoyin 'Yan Nijar Kan Yanke Yarjejeniyar Soji Da Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00

In ba a manta ba, a watan Fabrairun da ta gabata ne Hukumomin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar ta kori wasu sojojin rundunar zaman lafiya ta kungiyar Tarayyar Turai a Sahel wato EUCAP-Sahel da ma shugabar kungiyar daga kasar

Wannan matakin da gwamnatin sojoji ta Nijar ta dauka na zuwa ne lokacin da ya rage watanni hudu wa'adin da hukumomin suka bai wa rundunar ta EUCAP Sahel na ficewa daga cikin kasar.

A cikin wasika da ministan cikin gida na kasar Nijar ya sanyawa hannu wacce ya aikewa shugaban rundunar Eucap Sahel reshen kasar Nijar ya sanar da baiwa wasu sojojin rundunar su 15 sa'o'i 72 domin ficewa daga cikin kasar ta Nijar bisa zargin su da shigowa cikin kasar ba bisa ka’ida ba kuma sun shigo ba tare da sun sanar da mahukunta ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG