Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dole Amurka Ta Inganta Hulda Da Kasashen Afirka Don Tabbatar Da Samun Muhimman Ma'adanai- USIP


Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden

Cibiyar samar da zaman lafiya ta Amurka ta bayyana cewa. dole ne Amurka ta inganta huldar kasuwanci da kasashen Afirka domin dakile dogaro ga kasar China wajen samun ma'adanai masu mahimmanci.

WASHINGTON, D. C. - Cibiyar ta Amurka ta bayyana a cikin wani rahoto cewa, "Tsaron tattalin arzikin Amurka da na kasa ya dogara ne kan samar da ingantaccen, wadataccen ma'adanai masu mahimmanci, ciki har da na Afirka."

Amurka ta ce, ta na dogaro ne kan “kasashen waje da ke da tasiri”, musamman akan kasar China, kan muhimman ma’adanai masu mahimmanci, ta ce, kuma dole ne su samo wasu hanyoyin samun kayayyaki don gujewa takaitawa da kuma fuskantar barazanar daga China kan fitar da kaya.

Kamfanonin hakar ma'adinai na yammacin Turai suna kokarin bin sahun kasar China a tseren na ganin an samar da albarkatu masu yawa a Afirka, muhimman sassa daga kera motocin lantarki zuwa masana'antun tsaro.

Don kokarin cimma China da ta riga ta yi gaba a rige-rigen a Afirka, dole ne Washington ta fitar da "karin tsarin diflomasiyyar kasuwanci masu maida hankali kan gina muhimmin hadin gwiwa na ma'adinai a Afirka," in ji rahoton mai shafuka 76.

Wani zabi ga Amurka shine habaka diflomasiyyar kasuwanci a kasashe irin su Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, wadda ke kan gaba wajen samar da cobalt a duniya, da Zambia, kasa ta biyu mafi girma a Afirka mai samar da tagulla, in ji shi.

Gasar tabbatar da samun ma'adanai a Afirka na kara zafi yayin da kamfanonin Gabas ta Tsakiya masu kudi suma suka shiga gasar.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG