Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar EFFC Za Ta Gurfanar Da Bobrisky Kan Laifin Wulakanta Takardar Naira


Bobrisky
Bobrisky

Hukumar EFCC a Najeriya ta kama Idris Okineye wadda aka fi sani da Bobrisky, bisa zargin wulakanta takardar Naira.

WASHINGTON, D. C. - Ana zargin Bobrisky ya watsa kudi a wurin bikin fitowar farko na fim din Ajakaju, da jaruma kuma furodusa Eniola Ajao ta yi, a Film One Circle Mall, da ke unguwar Lekki a Legas a watan jiya.

An kuma ta yada faifan bidiyon taron a shafukan sada zumunta. Shahararriyar wadda ke da mabiya sama da miliyan biyar a Instagram, har yanzu ba ce uffan ba.

Kakakin Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), Dele Oyewale, ya ce za a gurfanar da Bobrisky a kotu da zarar an kammala bincike, ba tare da bayar da wani lokaci ba.

A watan Fabrairu ne aka yanke wa wata ‘yar wasan kwaikwayo Oluwadarasimi Omoseyin hukuncin daurin watanni shida a gidan yari bisa laifin watsi tare da taka sabbin takardun kudin Naira.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG