Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tudun Biri: Sojojin Da Suka Kai Hari Bisa Kuskure Za Su Gurfana A Gaban Kotun Soji


Babban Hafsan Hafsoshin Rundunar Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa
Babban Hafsan Hafsoshin Rundunar Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa

Harin na ranar 3 ga watan Disambar 2023, na daya daga cikin kurakurai mafiya muni a hare-haren da jiragen sojin saman kasar suka kai kan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.

Wasu jami'an sojin Najeriya biyu, za su gurfana gaban kotun soji, saboda rawar da su ka taka, a harin jirgi mara matuki na watan Disamba, wanda ya hallaka farar hula akalla 85, a cewar Hedikwatar Tsaron kasar.

A ranar Alhamis hedkwatar sojin ta Najeriya ta bayyana hakan watanni bayan da ta sha alwshi za ta binciki harin.

Harin na ranar 3 ga watan Disambar 2023, na daya daga cikin kurakurai mafiya muni a hare-haren da jiragen sojin saman kasar suka kai.

Rundunar sojin Najeriya ta amsa cewa, jirgi mara matukin, ya yi barin wuta kan wani kauye da ake kira Tudun Biri bisa kuskure a jihar Kaduna ta arewa maso yamma, ya kashe mazauna wurin yayin da su ke bikin Maulidi.

Sojoji na amfani da hare-hare ta sama, wajen yakar mayaka masu tsattsauran ra'ayin addini, a arewa maso gabas, da kuma kungiyoyin sace mutane don neman kudin fansa, a arewa maso yamma.

Sun ce sun yi kuskuren zaton cewa taron, wata haduwa ce ta kungiyoyin miyagu, sannan suka nemi afuwa saboda wannan kuskuren.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG