A halin da ake ciki, Isra'ila na kokarin yi wa birnin Rafah kawanya, suna masu cewa birnin shi ne mabuya ta karshe ga mayakan Hamas.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sauka yau Alhamis a birnin Beijing domin gudanar da ziyarar aiki ta kwanaki biyu a kasar Sin, a wani mataki na nuna hadin kai tsakanin kasashen masu kama karya a yayin da Moscow ke ci gaba da kai sabbin hare hare a Ukraine.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a ranar Laraba ya yi watsi da sukarsa da ake yi cewa ba ya shirin fuskantar dahir a zirin Gaza bayan yaki, yana mai cewa ba zai taba yiwuwa a shirya wani yanayi a yankin Falasdinawa da ke fama da rikici ba har sai an fatattaki Hamas.
Taiwo ta rasu ne a watan Nuwamban shekarar 2023 sakamakon mumunan raunin da ta samu a kwakwalwar ta bayan afkuwar mumunan lamarin a gidan su da ke Newmarket.
A cikin kwanaki masu zuwa, ana sa ran sojojin Amurka da ke gabashin tekun Bahar Rum za su hada karshen daya gefen harabar wata dirkekiyar tashar jirgin ruwa - mai tsawon filayen wasan kwallon kafa na Amurka guda biyar a gabar teku a arewacin Gaza.
Mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka Kurt Campbell ya fada a ranar Litinin cewa gwamnatin Biden ba ta ganin akwai yuwuwar Isra’ila ta samu “cikakkiyar nasara” wajen fatattakar Hamas a yankin Gaza na Falasdinu.
Firaiminista Benjamin Netanyahu ya fada a ranar Alhamis cewa barazanar da Amurka ta yi na hana makamai ba za ta hana Isra’ila ci gaba da kai hare-hare Gaza ba, lamarin da ke nuni da cewa za ta iya yin gaban kanta wajen mamaye birnin Rafah mai cunkoson jama’a ba tare da goyon bayan babbar kawarta ba
Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce da sanyin safiyar Juma’a Yarima Harry zai gana da Babban Hafsan Hafsoshin rundunar tsaron Najeriya, Janaral Christopher Gwabin Musa.
Shugaba Joe Biden ya fada jiya Laraba cewa ba zai aika da muggan makamai ga Isra'ila da za ta iya amfani da su wajen kai hare-haren wuce gona da iri kan Rafah ba, wanda yake tungar karshe ta Hamas a Gaza, saboda nuna damuwa kan yadda zai afka kan fararen hula fiye da miliyan 1 da ke fakewa a wurin.
Duk da cijewar da tattaunawar Isira'ila da Hamas ta yi, Amurka na fatan bangarorin biyu za su cimma jituwa kan sauran bambancin da ke tsakaninsu don a samu tsagaita wuta.
Putin ya sake samun sabon wa’adin mulki na shekaru 6 a watan Maris din daya gabata bayan daya lashe zaben shugaban kasar da aka yi ba tare da wata hamayya ba.
Kungiyar mayaka ta Falasdinu a jiya Litinin ta amince da shawarar tsagaita bude wuta a Gaza daga masu shiga tsakani, sai dai Isra'ila ta ce sharuddan ba su biya bukatunta ba, kuma za ta ci gaba da kai hare-hare a Rafah yayin da take shirin ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar.
Domin Kari
No media source currently available
Ma’aunin matsalar cin hanci da rashawa a Zambia ya nuna cewa kasar ta samu ci gaba a karon farko cikin shekaru goma, kamar yadda kungiyar Transparency International a kasar ta sanar. Hukumomi a kasar sun ce kwalliya ta fara biyan kudin sabulu a dagewar da suka yi wajen karfafa bin doka da oda.
A lokacin da Martha Ngoye take aiki a matsayin babbar jami’ar al’amuran shari’a a hukumar sufurin jiragen kasa ta Afirka ta Kudu, ta kwarmata badakalar kwangilolin gwamnati na miliyoyin kudi da aka bayar ba bisa ka’ida ba. Sai dai a maimakon a sakanya mata da alheri, sai aka kore ta a wurin aiki.
Kungiyoyin tabbatar da ka’ida a hada-hadar tattalin arziki a Malawi sun yi kira ga gwamnatin kasar da ta magance wasu matsaloli da ke tattare da tsarin bayar da kwangiloli na kasar.Wani rahoto a 2021 ya nuna cewa harkokin bayar da kwangiloli na gwamnati a kasar suna dabaibaye da cin hanci da rashawa
Hukumomi a Najeriya sun daura damarar yaki da magudin zabe, a wani muhimmin lamari ga dimukradiyya a Afirka. Bayan babban zaben 2023, Najeriya ta fara daukan matakan hukunta wadanda aka samu da laifin magudin zabe domin dawo da martabar tsarin zabe a kasar.
A farkon wannan shekarar, kungiyar dake fafutukar yaki da cin hanci ta kasa da kasa, Transparency International, cikin rahotonta na 2023, ta ce yaki da matsalar cin hanci da rashawa a Afirka ya fuskanci koma-baya sosai, inda a wasu kasashen, babu wani abu da aka cimma a game da haka.
Hukumomi a Najeriya su na duba yiwuwar bullo da jami’an ‘yan sanda mallakin jihohi a fadin kasar a wani bangare na magance hare-haren ‘yan bindiga, da garkuwa da mutane da kuma ‘yan fashin daji. ‘Yan Najeriya dai sun yi maraba da wannan yunkuri, sai dai suna cike da shakku.